Wata Sabuwa Ana Zargin Gwamnatin Sokoto Da Cin Zarafin Jami'an Tsohuwar Gwamnatin Jihar


Jami’an tsohuwar Gwamnatin jihar Sokoto ta Aminu Waziri Tambuwal sun zargi gwamnati mai ci da fakewa da batun bincike wajen cin zarafi da yi musu bita-da-ƙullin siyasa.

Hakan dai ya biyo bayan kamen da suka ce jami’an tsaron sun yi wa wasu tsoffin kwamishinoni ana tsaka da bukukuwan Sallah da sunan za a bincike su.

Sabuwar gwamnatin Sokoton dai ta kafa kwamitoci daban-daban domin binciken gwamnatin da ta gada ciki har da wanda zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta Aminu Waziri Tambuwal ta yi gwanjon wasu daga cikin kadarorin gwamnati a jihar.

Sai dai bayan da kwamitin mai mutum 19, ya soma aikinsa na bincikar yadda tsohuwar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi gwanjon kadarorin da suka haɗa da manyan motocin alfarma da sauran su, ake ta samun korafe-korafe daga ɓangaren tsohuwar gwamnatin.

Alhaji Isa Bajini Galadanci, kwamishinan muhalli ne a lokacin tsohuwar gwamnatin ya shaida wa BBC cewa ba maganar ƙwace motoci ne ke damunsu ba, yadda ake wulaƙanta su da cin zarafinsu shi ne abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

Ya ce ''a yanzu alal misali sun kama mu mu uku, da ni da tsohon shugaban ma'aikata da tsohon kwamishin tsaron cikin gida, ba tare da gayyatarmu ba''.

''Kamar ni, na gama yankan ragunana (Layya) kenan, sai ga motoci kusan biyar da 'yan sanda da bindigogi suna harɓin iska, yadda ka san mutum ya kashe shugaban ƙasa.Kana tare da mutane cikin mutuncinka a zo a yi maka wannan'', in ji tsohon kwamishinan.

Ya yi zargin cewa ɓata suna ne da cin zarafi da kuma wulaƙanci gwamnatin jihar ta yi musu, yana mai cewa gwanjon motocin aka yi musu suka saya, kuma suna da takardun shaida da ke nuna cewa sayen motocin suka yi.

To amma gwamnatin jihar Sokoton, ta bayyana cewa babu wani abu da suka yi da ya saɓa wa doka, kamar yadda Malam Abubakar Bawa mai bai wa gwamnan jihar shawara kan kafafen yaɗa labarai ya shaida wa BBC.

''Maganar cewa an yi musu gwanjon motocin bisa ƙa'ida ba haka take ba, ba muna cewa ba a yin gwanjo ba ne, amma akwai matakai da ya kamata a bi wajen yin gwanjon kayan gwamnati'', in ji Mallam Bawa.

Ya kuma musanta batun cewa sun tura jami'an tsaro domin cin zarafin jami'an tsohuwar gwamnatin.

Jim kadan bayan hawansa kan kujerar gwamnan jihar a ƙarshen watan Mayu, Gwamnan Ahmad Aliyu na jihar ta Sokoto ya sanar da rusa duk wasu naɗe-naɗen mukamai da wanda ya gada Aminu Waziri Tambuwal ya yi ciki har da na sarautun gargajiya.

Sannan kuma ya kakkafa kwamitoci daban-daban da za su binciki tsohuwar gwamnatin ta fuskoki daban-daban.

No comments