Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa EFCC Na Neman Matar Emefiele Ruwa A Jallo

Hukumar da ke Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon-ƙasa ta EFCC ta ayyana neman matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ruwa-a-jallo.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar ta ce tana neman Margaret Dumbiri Emefiele, tare da wasu mutum uku bisa laifukan da suka shafi almundahanar kuɗi.

Sanarwar ta ce hukumar na zargin mutanen huɗu da laifin haɗa baki da tsohon gwamnan babban bankin wajen karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗen gwamnatin Tarayya.

Tun bayan kama Mista Emifeile ne dai rahotonni ke cewa matar tasa ta riƙa ɓoye kanta.

Sauran mutanen da hukumar ke nema sun haɗar da wani jami'an babban bankin ƙasar CBN, mai suna Eric Odoh, da Anita Omoile wata 'yar ƙasuwa da kuma Jonathan Omoile wani jami'i a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.

Hukumar ta buƙaci 'yan ƙasar da su taimaka mata da bayanan da za su kai ga kama mutanen duk inda aka gansu.

Tun bayan datakar da tsohon gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, yake ci gaba da tsare a hannun hukumomi bisa zargin almundahanar kuɗi.

Madoga BBC Hausa.

No comments