Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero Koma Jam'iyyar APC
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya koma jam'iyyar APC, watanni kaɗan bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Ramalan Yero ya sanar da ficewar tasa ne a wani bayani da ya yi wa manema labaru, yau Litinin a garin Kaduna.
A bayanin nasa, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya koma APC ne bisa dalilai na ƙashin kansa bayan ya tattauna da waɗanda ke kusa da shi a harkar siyasa.
A cikin watan Oktoban shekarar 2023 ne Yero ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Ramalan Yero ya riƙe gwamnan jihar Kaduna ne ƙarƙashin jam'iyyar PDP daga shekara ta 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Patrick Yakowa a wani hatsarin jirgin helikwafta.
Daga nan ne ya yi takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inwar jam'iyyar ta PDP sai dai bai yi nasara ba,
Daga baya Ramalam Yero ya sha yunƙurin sake yin takarar gwamnan jihar, sai dai bai samu nasarar hakan ba, inda ya gaza yin nasara tun a matakin zaɓen fitar da ɗan takara.
Madoga BBC Hausa.
No comments
Post a Comment