Hukuncin Kotun Ƙoli Mataki Ne A Tafarkin Da Ya Dace Kuma Babban Gyara Ne Da Kuma Cigaba A Sassan Ƙasar
Jagoran adawa a Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce hukuncin da Kotun ƙoli ta zartar kan tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi babbar nasara ce ga ƴan Najeriya.
Atiku ya yaba da hukuncin ne a bayanin da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
Atiku ya ce hukuncin Kotun Ƙoli mataki ne a tafarkin da ya dace kuma babban gyara ne ga tabbatar da ci gaba a sassan ƙasar.
Jagoran adawar ya ce matakin haɗa kason kuɗaɗen jiha da na ƙananan hukumomi ya samo asali ne daga son rai na siyasa.
"Na goyi bayan matakin Kotun Ƙoli cewa tsarin gwamnati ya kafu ne a mataki uku, kuma ƙananan hukumomi ne ya kamata su kasance cibiyar tabbatar da ci gaba," a cewar Atiku.
Ya ƙara da cewa hatta kuɗaɗen shiga da ƙananan hukumomin ke samarwa su kasance sun tafi kai-tsaye zuwa asusunsu
No comments
Post a Comment