DSS Ta Bayar Da Belin Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayar da belin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC).

Hukumar ta sanar da bada belin Kwamared Joe Ajaero, da misalin karfe 11:25 na dare, da ‘yan mintuna kadan.

Bayan da magoya bayan shugaban kungiyar kwadagon suka yi barazanar kulle ko Ina a kaf fadin Nijeriya matukar jami'an basu saki shugaban kungiyar kwadagon ba.

An kama Ajaero da safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe International Airport, Abuja, akan hanyarsa ta zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.

No comments